ABNA24 : Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa a ranar Lahadi 17 ga watan yuli da muke ciki ne wasu kamfanonin kasa da kasa suka a yayin bincike suka tabbatar da cewa sun taimakawa yahudawan wajen aikin satar bayanai a wayoyin shuwagabannin kasashen duniya da manya –manyan mutane da kuma wasu fitattun mutane a duniya.
A jiya jumma ce ma’aikatar harkokin wajen Pakistan ta zargi kasar india da amfani da irin wadan nan ayyukan leken asiri.
Labarin ya kara da cewa al-amarin ya shafi shugaban kasar Faransa da ministocinsa wadanda suka canza wayoyi da lambobinsu a jiya.
342/